in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnmatin Najeriya ta bukaci sassa masu zaman kansu da su taimaka wajen fadada tattalin arzikin kasar
2016-08-05 09:36:50 cri
Gwamnatin Najeriya ta bukaci sassa masu zaman kansu da su ba da tasu gudummawar a kokarin da ake na fadada sassan tattalin arzikin kasar.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya Udoma Udo Udoma ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a taron dandalin tuntubar juna na masu ruwa da tsari game da yadda za a fasalta kasafin kudi na matsakaicin lokaci (MTEF) daga shekarar 2017 zuwa 2019, wanda ya gudana a birnin Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya.

Da ya ke karin haske game da yadda za a aiwatar da dabarun kasafin kudin a zahiri, minista Udoma ya bukaci sassan masu zaman kansu da su hada kai da gwamnatin tarayya ta yadda za a aiwatar da canje-canjen da suka dace a bangaren tattalin arzikin kasar.

An shirya taron ne da nufin ilimantar da 'yan Najeriya game da manufofin gwamnati ta fuskar tattalin arziki da kuma kasafin kudin kasar na wannan shekara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China