in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun harbe mayakan Boko Haram goma
2016-06-25 12:43:14 cri
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda goma da ake zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne a jihar Borno, dake arewa maso gabashin kasar, bayan wani kwaton bauna da suka ci nasarar yi musu a kauyen iyaka na Gamboru-Ngala.

Janar Lucky Irabor, komandan shirin aikin Lafiya Dole, ya yi wannan sanarwa a yayin wani taron manema labarai a Maiduguri, babban birnin Jihar.

Janar Irabor ya kara da cewa rundunar ta samu babban nasara a cikin wannan aiki na kakkabe yankunan daban daban na jihar.

A cewar komandan din, sojojin sun kama manyan bindigogi AK47 guda shida, harsasai, katon guda na igiyar ta da boma bomai da kuma wani kundin dake bayani kan yadda ake kera nakiyoyin dake fashewa nan take, yayin wannan hari.

Haka kuma sojojin sun tsirar da rayukan mata biyu, 'yan mata biyu da yara uku, in ji mista Irabor.

Rundunar sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram biyu da kuma kwato kauyuka goma sha daya daga hannun mayakan kungiyar a ranar 8 ga watan Juni, bayan sun gudanar da sintirin yaki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China