in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun mika mutane 65 da suka ceto ga hukumomin arewa maso gabashin kasar
2016-05-07 12:16:51 cri
Rundunar sojan Najeriya ta fada cewar a Juma'ar data gabata ne ta damka mutane 65 wadanda mata ne da kananan yara, wadanda ta ceto su daga hannun mayakan Boko Haram, bayan wani simame da suka kaddamar a mafakar mayakan a dajin Sambisa dake jahar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Birdediya janar Victor Ezugwu, babban kwamandan runduna ta 7 na sojojin kasar ne ya jagoranci mika mutane ga gwamna Kashim Shettima na Borno a birnin Maiduguri.

Ezugwu yace, mutanen da aka ceto, sun hada da mata 38 da kananan yara 27, kuma an samu nasarar ceto su ne bayan da sojojin kasar suka yi galaba a kan mayakan na Boko Haram a yayin wani sumamen da dakarun kasar suka kaddamar.

Ya kara da cewar, biyu daga cikin mata 'yan asalin jamhuriyar Kamaru ne, yayain da ragowar 'yan Najeriya.

Rundunar sojin Najeriyar ta fada cewar, ta yanke shawarar mika mutanen ne ga gwamnatin jahar Borno domin a yi musu bita kafin a mayar da su don cigaba da rayuwa cikin alummomin su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China