in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Maurice, kasar Afrika ta farko a jerin hukumomin gwamnati dake aiki da fahasar zamani ta Digital
2016-08-10 10:30:13 cri

Maurice ta kasance kasar Afrika ta farko ta fuskar hukumomin gwamnati dake aiki da fasahar zamani ta Digital (e-Government), a cewar wani sakamakon jerin kasashe na MDD kan binciken e-Government a shekarar 2016.

Maurice na samun ci gaba har ma a matakin duniya inda ta wuce matsayi na 76 a shekarar 2014 zuwa matsayi na 58 a binciken baya-bayan da ya shafi kasashe 193 na kasashe mambobin MDD.

Binciken ya shafi auna karfin wata kasa na kafa tsarin e-Government, ta hanyar amfani da fasahohin sadarwa na kirkire-kirkire a cikin hukumomin gwamnati, domin taimakawa wajen aiwatar da cimma maradun ci gaba cikin karko guda 17, da suka kasance kuma tushen ajandar 2030.

Da yake nuna farin cikin da wannan kwazo na tsibirin Maurice, Etienne Sinatambou, ministan kimiyya da fasaha na kasar Maurice ya bayyana kafa a kalla sabbin ayyukan gwamnati guda 50 a kan shafukan internet domin sabuwar shekarar kasafin kudi wato Yulin shekarar 2016 zuwa Yunin shekarar 2017. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China