in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake maida faraministan Mauritaniya kan kujerarsa
2014-02-04 16:40:16 cri
Faraministan kasar Mauritaniya da ya gabatar da murabus a ranar Lahadi, ya sake maida komawa kan mukaminsa bayan wani kudurin da shugaban kasar Mauritaniya ya sanya ma hannu a ranar Litinin da yamma a birnin Nouakchott.

Sanarwar fadar shugaban kasar ta nuna cewa bisa kudurin da shugaban kasa ya rattabawa hannu a wannan rana, an nada dokta Moulaye Ould Mohamed Laghdaf a matsayin faraministan kasar Mauritaniya.

Faraministan da aka sake maida wa kan kujerarsa ya gana da shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz, wanda kuma ya umurce shi da ya kafa wata sabuwar gwamnati.

"Shugaban kasa ya karrama ni bisa sake nada ni faraminista, ya kuma umurce ni da na kafa gwamnatin ba da jima wa ba, gwamnatin da za ta amsa muhimman bukatun jama'a, ta hanyar kafa guraben aikin yi da tsaron cimaka", in ji mista Laghdaf a gaban manema labarai bayan wannan ganawa.

Wannan murabus na faraministan Mauritaniya wani cikon aikin ne bayan zabubukan 'yan majalisun da aka gudanar da jam'iyyar dake mulki ta lashe, bayan da bangaren 'yan adawa ya kauracewa zaben. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China