in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mauritaniya : Har yanzu akwai takaddama tsakanin masu mulki da 'yan adawa
2015-10-05 18:26:06 cri
Wani sabon kokarin da gwmnatin Mauritaniya take yi na sake maido da shawarwari tare da bangaren 'yan adawa na cikin mawuyacin hali, a cewar masu fashin baki. A tsakiyar watan Satumban da ya gabata, gwamnatin Mauritaniya ta bullo da wani shirin tuntubar juna na share fage ga tattaunawar kasa tsakanin masu mulki da 'yan adawa. Wannan tattaunawa ba ta samu karbuwa daga bangaren 'yan adawa masu kaifin ra'ayi ba, da suka janye daga shawarwarin shirye shirye, da ya kamata a bude a ranar 12 ga watan Oktoba mai zuwa, a cewar wata sanarwa da gwamnatin Mauritaniya ta aike wa daukacin jam'iyyun siyasa na kasar. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China