in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ya gana da shugaban kasar Mauritaniya
2014-08-03 16:52:54 cri

Da yammacin jiya Asabar ne zababben shugaban kasar Muritaniya Mohamed Ould Abdul Aziz, ya yi rantsuwar kama aiki a birnin Nouakchott hedkwatar kasar, bayan da ya sake lashe zaben shugabancin kasar ta Mauritaniya da ya gudana.

Bikin rantsuwar ta sa dai ya samu halartar shugabannin kasashe da dama, ciki hadda na Mali, da Senegal da Chadi, da ma wakilai fiye da 30 na gwamnatocin kasashe daban-daban, da na kungiyoyin kasa da kasa, wadanda suka halarci bikin, a wani filin motsa jiki na sada zumunci da kasar Sin ta ba da taimako wajen gina shi.

Ita ma manzon musamman ta shugaban kasar Sin, Madam Li Bin ta halarci bikin tare da mika masa kyakkyawar fata.

A daya gangaren, shugaba Aziz ya gana da Li Bin a fadarsa, inda wakiliyar ta shugaban kasar Sin ta isar da sahihiyar gaisuwa da fatan alheri daga shugaba Xi, tana mai cewa shugaban na Sin na dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar sada zumunci, ta hadin kai tsakanin Sin da Mauritaniya. Har ila yau Sin tana fata kara hadin kai da kasar, a fannoni daban-daban, ta yadda za a ciyar da dangantakarsu gaba.

Madam Li ta kara da cewa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta samu ci gaba mai ma'ana a nan gaba, duba da yadda shugabannin suke mai da hankali kan raya ta.

Da yake mai da jawabi, shugaba Aziz, ya bayyana godiya ga zuwan wakilin shugaban kasar Sin kasar sa, tare da mika sahihiyar gaisuwa ga shugaban Xi, ya na mai cewa Sin da Mauritaniya na da zumunci mai inganci. Kuma kasar sa na godiya kwarai ga taimakon da Sin take ba ta tsahon lokaci, tare da fatan kara yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a dukkanin fannoni, da ma ingiza dangantakar kasashen biyu zuwa matsayi na gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China