in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta kafa cibiyoyin kula da matan da rikice rikice ya shafa
2016-08-01 10:34:54 cri
Gwamnatin Najeriya za ta kafa cibiyoyin tallafawa matan da rikice rikice ya shafa a dukkan shiyyoyi 6 dake fadin kasar.

Ministar al'amurran mata da ci gaban al'umma Aisha Alhassan, ta tabbatar da hakan a garin Jalingo na jahar Taraba a arewa maso gabashin kasar, a lokacin da take karin haske game da nasarorin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta cimma a cikin shekara gudar da ta gabata.

Ta ce manufar bullo da wannan shirin shi ne, domin magance matsalolin yawaitar cin zarafin mata da ake samu a kasar, da kuma kula da matan da matsalolin suka shafa.

Aisha ta ce, ma'aikatar tana kokarin ganin an samar da wasu dokoki da suka shafi yaki da cin zarafin mata da kananan yara a dukkan jahohin kasar 36. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China