Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jahar El-Mustapha Sani ya fada kamfanin dillancin labarun Xinhua cewar, marigayi Moin Amsuri, wani malamin lissafi ne dake aiki a kwalejin Prestigious Nagarta dake Sokoto, kuma wasu 'yan bingida da ba'a san ko su wane ne ba suka hallaka shi a ranar Alhamis da ta gabata.
Sani ya fada cewar ana zargin wadanda suka hallaka shi 'yan fashi ne, kasancewar sun yi awun gaba da motarsa kirar Toyota.
Ya ce rundunar 'yan sandan jahar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bankado wadanda suka aikata wannan mummunan aiki, domin gurfanar da shi a gaban shari'a.
Shi dai marigayi Amsuri, ya koyar da darasin lissafi a makarantun jahar da dama sama da shekaru 30 da suka gabata. (Ahmad Fagam)