Mista Buhari ya ba da wannan tabbatancin a ranar Litinin a Abuja, hedkwatar Najeriya, a lokacin da ya karbar wata tawagar MDD dake karkashin wani manzon musamman na sakatare-janar, Mohammed Ibn Chambers.
Shugaban Najeriya ya tabbatar da cewa Najeriya ba za ta yi abin da zai kawo cikas ba ga aikin kwamitocin kan iyaka daban daban na MDD.
Bayan amincewa da shari'ar CIJ, a shirya muke na tabbatar da tsaro da kayayyaki ga kwamitin hadin gwiwa na tsakanin Kamaru da Najeriya (CNMC) domin gudanar da aikin shata layin kan iyaka, in ji shugaba Buhari.
Shugaban Najeriya ya bukaci dukkan kwamitocin da a ba su umurnin tafiyar da ayyukansu kamar yadda matakin CIJ ya tanada.
Da farko, Ibn Chambers, dake kuma shugaban CNMC, ya sanar da shugaba Buhari cewa kan kilomita 2100 dake raba Nijeriya da Kamaru, an shata 2001. (Maman Ada)