in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen IGAD na bukasa wata dabarar yaki da ta'addanci ta hadin gwiwa
2016-08-09 11:43:12 cri

Kasashe mambobi na hukumar kasa da kasa kan ci-gaba (IGAD), tare da kasar Tanzaniya, sun dauki niyya a ranar Litinin na bullo da wata dabarar shiyya ta hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci, in ji wasu manyan jami'ai a ranar Litinin.

Sakataren zartarwa na kungiyar IGAD, Mahboub Maalim, ya bayyana a yayin wani dandali kan tsaro a Nairobi cewa, dabarar shiyya ta rigakafi da kuma yaki da tsattsauran ra'ayi ta zama wajibi domin matsalar ta'addanci ta kasance wata annoba ga shiyyar da ma duniya. Dalilin haka ne, tsare-tsare da dokokin cikin gida ba su wadatu ba domin hana hare-haren ta'addanci, lamarin dake nuna bukatar wata dangantakar shiyya, in ji mista Maalim a yayin wani zaman taron tuntubar juna na bangarori daban daban masu ruwa da tsaki na Kenya kan bunkasa dabarar shiyyar gabashin Afrika domin yin rigakafi da yaki da kaifin kishin addini.

Babbar sakatariyar dake kula da harkokin wajen Kenya, Monica Juma, ta bayyana a nata bangare cewa, dabarun cikin gida na yaki da ta'addanci dole su taimaka wajen karfafa dangantakar hadin gwiwa tsakanin matakai daban daban kan dabarun cikin kasashe da na shiyoyi. Ganin babbar barazanar kaifin kishin addini da muke fama da ita a wannan lokaci, ke nan dabarun yaki da ta'addanci na bukatar wata fahimta kan yadda wannan matsala take karuwa, in ji madam Juma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China