Sakatare mai kula da harkar Ilimi a fadar shugaban kasar Kenya, Dr Fred Matiangi ya ce, likitocin nahiyar suna kaura zuwa kasashen yamma ne saboda karancin albashi da rashin kayayyakin bincike.
Matiangi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar yayin bude taron hadin gwiwa na shekara-shekara na ma'aikatan lafiya (MEPI) karo na 6 da aka gudanar a birnin Nairobin kasar Kenya. Ya ce, kasashen Habasha, Kenya, Malawi, Najeriya, Afirka ta kudu,Tanzaniya,Uganda,Zambia da Zimbabwe sune suka fi hasarar kudade, sakamakon kaurar da likitocin kasashen suka yi zuwa kasashen waje. Yayin da a daya hannun kuma, kasashen Australia da Canada da Burtaniya da Amurka suka fi amfana wajen daukar irin wadannan likitoci da da ma can suke da kwarewa.
Taron na kwanaki uku ya hallara masu ruwa da tsaki a fannin ilimin likitanci daga ciki da wajen kasar, da wakilan makarantun horas da ma'aikatan lafiya daga kasashen Afirka, wakilan cibiyoyin da ke daukar nauyi da sauran abokan hulda wadanda ke horas da ma'aikatan kiwon lafiya da raya harkokin bincike a kasashen yammacin Afirka.(Ibrahim)