in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU ta kara wa'adin takunkuminta a kan shugaban kasar Zimbabwe da wata shekara daya
2016-02-18 10:18:42 cri

Kungiyar tarayyar Turai EU ta kara wa'adin takunkumin da ta kakaba ma shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da Uwargidan shi Grace na wata shekara daya, sai dai jam'iyya mai mulkin kasar ta yi watsi da wannan mataki, tana mai bayyana shi a matsayin abin da bai halarta ba kuma dole a cire shi.

Kamar yadda shawarar da majalissar kungiyar ta amince da ita kuma jakadanta dake kasar Zimbabwe Philippe Van Damme ya gabatar a ranar Larabar nan, wannan matakin zai ci gaba da aiki a kan Shugaba Mugabe da Uwargidan shi, da kuma hukumomin tsaro sannan kuma za'a dakatar da takunkumin a kan wadansu manyan jami'ai guda biyar na bangaren tsaro.

Jakadan na kungiyar EUn ya kara da cewa, takunkumin makamai a kasar na nan daram, sannan za'a dakatar da matakan da aka saka ma manyan jami'an tsaron kasar.

EU ta ce ta kuma cire takunkumi a kan jami'ai na hannun daman Mugabe su 78.

Simon Khaya Moyo babban jami'i a jam'iyya mai karagar mulkin kasar kuma kakakin jam'iyyar ya musanta duk shawarar da kungiyar ta EU ta yanke, yana mai cewa ba sa bisa doka.

Ya ce, dole ne a cire takunkumin gaba daya da suka hada da na Shugaba Mugabe da Uwargidan shi, ya ce ba za'a tsaya kokarin tabbatar da halarcinsu a ko wane bangare ba, dole ne kawai a cire su gaba daya.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China