in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bude asibiti mai zaman kansa na farko a kasar Angola
2015-06-10 11:21:01 cri
Kasar Sin ta bude asibiti mai zaman kansa na farko a birnin Luanda dake kasar Angola. An dai gudanar da bikin bude asibitin ne a ranar Litinin, wanda kuma aka sanyawa suna "Zhongyan".

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin gine-gine na Zhongxing dake da helkwata hedkwata a lardin Jiangsu na kasar Sin ne ya gina asibitin.

Bikin bude wannan asibiti ya samu halartar ministan kiwon lafiya na kasar Angola José Van-Dúnem, da gwamnan jihar Luanda Graciano Francisco Domingos, da kuma sauran al'ummar kasar da dama.

Yayin bikin, ministan kiwon lafiya na kasar Angola Mr. Van-Dunem ya bayyana cewa, yankin da aka gina wannan asibiti na Zhongyan na da tarin jama'a, sai dai akwai karancin kayayyakin da ake bukata na kiwon lafiya masu inganci. Don haka a cewar sa asibitin Zhongyan zai biya bukatun kula da lafiyar jama'ar yankin. Kuma mazauna yankin da gwamnatin wurin, sun yi matukar farin ciki da ganin aka kafa asibitinshi, tare da fatan asibitin zai samu nasarar gudanar da managartan ayyuka a kasar ta Angola.

An ce, babban ginin asibitin mai hawa 3 ya da kayayyakin dake ciki sun lashe kudi har dala miliyan 10. Kuma yanzu haka akwai ma'aikatan kiwon lafiya fiye da 100 da suka zo daga kasar Sin, da Cuba, da Angola, wadanda ke gudanar da ayyuka a asibitin. Kaza lika cikin asibitin akwai gadaja gadaje 87, da sashen kula da yara kanana, da na mata, da sashen fida, da na jinyar marasa lafiya da dai sauransu.

Bugu da kari asibitin ya riga ya samu takardar shaidar izinin fara gudanar da aiki, ta ma'aikatar kiwon lafiyar kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China