Manuel Domingos Vincente ya yi wannan kiran a jiya lokacin da yake jawabi a rana ta hudu na babban taron muhawara na MDD.
Ya ce, matsalar canjin yanayi tana daya daga cikin kalubalen da dan-Adam ke fuskanta a wannan duniya, don haka kamata ya yi masu ruwa da tsaki a taron Paris kan canjin yanayi, su yi kokarin bullo da matakan da za su kasance masu tasiri ga kasashe masu tasowa.
MDD ce za ta jagoranci kokarin da kasashen duniya ke yi na ganin an cimma yarjejeniyar yaki da matsalar sauyin yanayi a taron na Paris. (Ibrahim Yaya)