Kwamitin shirya wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing ya fara tara fasalin bajon gasar

Jiya Lahadi 31 ga watan Yuli, rana ce ta cika shekara daya da biranen Beijing da Zhangjiakou suka cimma nasarar samun damar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a shekarar 2022. A daidai wannan lokaci, kwamitin shirya gasar ya gudanar da aikin "Aika da goron gayyata daga babbar ganuwa" a yankin Yanqing na birnin Beijing, da zummar neman tara fasalin bajon gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da na gasar nakasassu a shekarar 2022 daga jama'ar kasashe daban daban. A sa'i daya, tashar yanar gizo ta gasar wasannin biyu ta fara aiki a hukumance bisa adreshinsu na www.beijing2022.cn.
An ba da labari cewa, domin samun bajon gasanni mai kyau, za a gudanar da aikin tara fasalin bajon daga ranar 31 ga watan Yuli zuwa ranar 30 ga watan Nuwamban bana.(Fatima)