in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan Sin za su yi iyakacin kokari wajen cimma nasarori a gasar Olympics ta Rio
2016-07-21 20:18:18 cri

'Yan wasan motsa jiki na kasar Sin, na cikin shirin cimma manyan nasarori, yayin gasar Olympics ta birnin Rio da za a bude a watan Agusta mai zuwa.

Mr. Gao Zhidan, kusa a hukumar wasannin kasar ta Sin, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, gudanar gasar ta wannan karo a nahiyar kudancin Amurka, zai zame wa 'yan wasa da jagororin tawagar kasar ta Sin wani sabon yanayi na nuna hazakarsu.

Mr. Gao wanda shi ne zai jagoranci tawagar 'yan wasa da jami'an kasar ta Sin su 711 zuwa wannan gasa, ya ce, Sin za ta isa gasar ne da 'yan wasa 416, wadanda za su shiga rukunoni 210 cikin wasanni sama da 26.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China