Jam'iyya mai mulki a Burkina Faso ta lashe kujerun da dama a zaben kananan hukumomin kasar
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Burkina Faso ta bayyana cewa, kwarya-kwaryar sakamakon zaben da ta fitar ya nuna cewa, jam'iyyar MPP mai mulkin kasar ce ta lashe galibin kujerun da aka yi takara kansu a zaben kananan hukumomin kasar da ya gudana ranar Lahadin da ta gabata.
Alkaluma na cewa, a daren ranar Laraba, jam'iyyar ta lashe kashi 58.91 cikin 100 na kujerun da aka fafata a kansu a mazabu 363, wato kwatankwacin kujeru 11,167.
Hukumomin wucin gadin kasar ce dai suka rusa majalisun kananan hukumomin da tun farko suke hannun jam'iyyar Compaore.(Ibrahim)