in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Burkina Faso za su kammala sauraron batutuwan da suka shafi juyin mulki kafin karshen wannan shekara
2016-06-07 20:35:25 cri
Kwamishina a gwamnatin kasar Burkina Faso Alioune Zanre ya bayyana cewa, za a kammala sauraron kararrakin da suke da nasaba da yunkurin juyin mulkin kasar na ranar 16 ga watan Satumban shekarar 2015 kafin karshen wannan shekara.

Jami'in ya ce ana zargin mutane 75 da hannu a lamarin, kuma yanzu haka ana tsare da mutane 50 daga cikinsu, yayin da aka ba da belin mutane 17 kana akwai mutane 8 da ba a tsare su ba.

A ranar 16 ga watan Satumban shekarar 2015 ne wasu sojoji da ke gadin fadar shugaban kasar da ya gabata suka kifar da gwamnatin wucin gadin kasar na dan wani lokaci, kafin daga bisani masu zanga-zanga da jami'an sojojin kasar su hambarar da su.

Bayan juyin mulki ne kuma aka kama sojoji da fararen hula da dama wadanda ke goyan bayan tsohon shugaba Blaise Compaore bisa zargin su da hannu a juyin mulkin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China