Ramaphosa, ya bayyana hakan ne a lokacin gudanar da bikin Sallar Idi ta wannan shekarar a Laudium, yammacin Pretoria, ya ce ya zama tilas a yi aiki tare da juna domin yakar laifuka da suka shafi ta da rikicin addini da wariyar launin fata da kuma aikata fyade.
Ramaphosa, ya ce ya zama wajibi al'ummar musulmi su hada kai wajen yin Allah wadai da yake-yake, da rikicin addini da ayyukan ta'addanci wadanda ke sanadiyyar hallaka rayukan al'umma, kuma su dage wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaban duniya baki daya.
Ya kara da cewar bayan kammala azumin watan mai tsarki, ya kamata a yi aiki tare wajen yakar talauci, da rashin daidaito, da rashin adalci, da yake-yake, da ayyukan ta'addanci wadanda ke sanadiyyar hallaka rayukan al'umma da ba su ji ba su gani ba.
Mataimakin shugaban kasar ya yabawa al'ummar musulmi dangane da rawar da suke takawa wajen sake ginawa kasa da kawo ci gaban kasar. (Ahmad Fagam)