Mai magana da yawun sashen hulda da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Afirka ta Kudu Clayson Monyela ya bayyana cewa, barazanar yiwuwar kai harin ta'addancin da Amurka ta bayar,bai gamsar ba,manufarci ne kuma babu wasu cikakkun shaidu.
A ranar 4 ga watan Yuni ne ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Pretoria, ya bayar da wata takardar gargadin yiwuwar kai harin ta'adainci kan muhimman wuraren da Amurke ke zuwa a Afirka ta kudu.
Sai dai gwamantin Afirka ta kudu ta zargi Amurka da rashin bin matakan da suka dace wajen bayar da gargadin yiwuwar kai harin ta'addancin.
Amma kuma ofishin jakadancin Amurka da ke Pretoria ya tsaya kai da fata cewa, akwai kamshin gaskiya kan gargadin da ya bayar.(Ibrahim)