Sudan ta Kudu: Shugaba Kiir ya canja mataimakin shugaban kasa na farko Machar
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sanya hannu kan wani kudurin shugaban kasa a ranar Litinin yamma, na sallamar mataimakin shugaban kasa na farko Rieck Machar. Shugaba Kiir ya zabi ministan ma'adinai Taban Deng Gai domin maye gurbin mista Machar, bayan ballewar wani reshen kungiyar kwato 'yancin Sudan dake cikin adawa wato SPLM-IO, tsofuwar kungiyar 'yan tawaye, wanda kuma ya zabi mista Gai a matsayin shugaban kungiyar, dalilin ficewar mista Machar daga Juba bayan tashe tashen hankalin da suka barke tsakanin dakarunsa da sojojin dake biyayya ga shugaba Kiir. Haka kuma, shugaba Salva Kiir ya kori ministan kudi David Deng Athorbei da nada ministan kasuwanci da masana'antu Stephen Dhieu Dau a kan wannan mukami. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku