Wani jami'i daga ma'aikatar harkokin wajen Kenya ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, ministocin zasu tattauna hanyoyin da za'a kawo karshen rikicin ne tsakanin dakarun dake biyayya ga shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir dana mataimakinsa Riek Machar.
Gamayyar kungiyar misnistocin tarayyar kasashen gabashin Afrika wato (IGAD), sun hada da na kasashen Djibouti, da Eritrea, da Ethiopia, da Kenya, da Somaliya, da Sudan, da Sudan ta kudun da kuma Uganda.
A wani cigaban kuma, Paul Malong Awan, babban jami'in dakarun 'yantar da jama'ar kasar Sudan (SPLA), ya gargadi bangarorin dakarun na Sudan ta kudu, dasu yi kaffa kaffa wajen afkawa fararen hula a Juba.
Malong yace, sojojin ba zasu laminci duk wani yunkurin na kai hari kan fararenm hula ba.
Kasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da barkewar sabon rikicin a Juba.(Ahmad Fagam)