in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin jihar Borno a Najeriya za ta kara samar da tsaro ga ma'aikatan agaji
2016-08-01 10:02:29 cri
Gwamnatin jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya za ta kara samar da adadin jami'an tsaro ga ma'aikatan bada agaji a jihar, sakamakon wani harin ta'addanci da aka kaddamar a kusa da ofishin jami'an ba da agaji na MDD a ranar Alhamis da ta gabata a kusa da birnin Maiduguri.

Da yake jawabi a yayin taron manema labarai a Maiduguri, mataimakin gwamnan jihar Borno Mamman Durkwa, ya fada cewar gwamnati ta damu matuka game da faruwar wannan lamari.

Ya kara da cewar, gwamnatin jihar za ta hada kai da sauran jami'an tsaro domin bada kariya ga ma'aikatan bada agajin, domin kare faruwar irin abin da ya faru a ranar Alhamis da ta gabata.

Durkwa ya yi Allah wadai da rahoton da kafafen yada labaru suka yada cewar, an kwashe wasu daga cikin ma'aikatan ofishin MDD dake jihar sakamakon faruwar wannan al'amari.

Mataimakin gwamnan ya ce, ya gana da jami'an jin kai na MDD, kuma sun tabbatar masa cewar, wannan hari ba zai sa su yi kasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukansu ba.

Ya ce, jami'an ba su da niyyar ficewa daga jihar sabanin yadda wasu kafafen yada labaru suka rawaito. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China