in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya Boko Haram na yin shigar bultu domin kubuta daga hannun sojojin kasar
2016-06-28 11:26:04 cri

Mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya sun yi badda kama a matsayin 'yan banga da maharba domin kaucewa farmaki daga sojojin kasar, rundunar sojin kasar ne ta tabbatar da hakan a jiya Litinin.

Cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a birnin Legas, mai magana da yawun hedkwatar tsaron kasar birgediya janar Rabe Abubakar, ya bayyana cewar rundunar sojin kasar ta gano mayakan na Boko Haram ne bayan wani samame da ta kai a maboyarsu dake dajin Sambisa.

Ya ce, mayakan sun bullo da wani sabon salo na yin shigar bultu a matsayin maharba ko 'yan kato da gora domin su samu nasarar tsallakewa daga hannun sojin kasar.

Ya kara da cewar, bayan maharani sun sulale daga dajin Sambisa suna ta yunkurin kaddamar da hare hare kan fararen hula inda suke sanya kaya irin na yan banga ko maharba a matsayin wata sabuwar hanya ta yaudara.

Rabe ya ce, irin hakan ta taba faruwa a kauyen Kuda-Kaya a yankin Madadali na jihar Adamawa, inda mayakan na Boko Haram suka sanya kaya irin na 'yan banga, kuma suka bude wuta kan jama'a a lokacin ana gudanar da biki a yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China