Asusun yara na MDD na UNICEF, ya bayyana dakatar da ayyukan bada agajin jin kai da MDDr ke gudanarwa a arewa maso gabashin Najeriya zuwa wani dan lokaci, bayan da wasu mahara da ba a tantance da ko su waye ba, suka kaiwa tawagar masu bada agajin hari, a kan hanyar su ta komawa Maiduguri daga garin Bama.
Sanarwar da asusun na UNICEF ya fitar ta bayyana cewa, wannan hari baya ga jami'an dake aikin na bada agajin jin kai, ya ma shafi al'ummun dake matukar bukatar tallafin, musamman wadanda ke fama da karancin abinci mai gina jiki.
A ranar Laraba ne shugaban hukumar bada agajin jin kai na MDD Stephen O'Brien, ya bayyana cewa matsalar jin kai da hare-haren Boko Haram ta haifar, ta janyo tashin hankali mai yawa ga Najeriyar da ma sauran makwabtan ta.
A 'yan watannin nan dai rundunar sojojin Najeriyar ta kaddamar da ayyukan soji da dama, domin murkushe kungiyar ta Boko Haram daga sassan da 'ya'yan ta ke samun mafaka.(Saminu Alhassan)