Rahoton ya kuma bayyana cewa, yawan mutanen da suke amfani da yanar gizo a kasar ta Sin ya kai kashi 51.7 cikin dari na al'ummar kasar, wanda ya zarce kashi 3.1 cikin dari na wannan adadi a duniya.
Bugu da kari, a sakamaon yaduwar wayar salula ta zamani, al'ummar Sinawa suna kara sha'awar yin amfani da wayar salula don shiga yanar gizo, har ma kashi 25 cikin dari na masu ziyartar yanar gizo a kasar su ke amfani da wayarsalula kawai don shiga yanar gizo. (Zainab)