Lu Wei, shugaban ofishin kula da al'amurran yanar gizo ta kasar Sin ya sanar da kammala babban taron din na yini uku.
A lokacin taron, shugaban kasar Sin Xi Jingpin ya bukaci dukkan kasashe da su mutunta ikon yanar gizo sanna a hada hannu tare wajen bada kariya na yanar gizon, a kuma hada hannu da zuciya daya a kuma inganta ikon yanar gizon.
Babban taron dai na yanar gizon internet ya samu ganin an rattaba hannu a kan jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwwa tsakanin Sinawa da kamfanonin sadarwa na zamani na kasashen waje. (Fatimah)