in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu ziyartar shafukan yanar gizo ta salula ya kai sama da miliyan dari 9 a Sin
2016-01-06 20:08:10 cri
A yau ne kungiyar masu kula da harkar yanar gizo ta kasar Sin ta fidda wani rahoton da ke bayani game da yanayin yanar gizo na kasar Sin na shekarar 2015 da kuma matakan bunkasa harkokin yanar gizo na kasar Sin a shekarar 2016, inda ta nuna cewa, ya zuwa watan Nuwamba na shekarar 2015, adadin masu ziyartar shafukan yanar gizo ta wayoyin salula a nan kasar Sin ya kai sama da miliyan 905, adadin da ya kai wani sabon matsayi.

Kungiyar ta gabatar da wannan rahoto ne a yayin taronta na shekara-shekara. inda babban sakataren kungiyar Lu Wei ya ce, a shekarar bana, za a ci gaba da inganta harkar yanar gizo, adadin masu yin amfani da fasahar yanar gizo ta 4G zai karu da miliyan dari biyu ko miliyan dari uku, kuma za a fara gwada amfani da fasahar yanar gizo ta 5G, domin kyautata harkokin yanar gizo na salula a nan gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China