in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron ministocin cinikayya na G20 na shekarar 2016 a Shanghai
2016-07-09 12:56:04 cri
Yau ne aka bude taron ministocin cinikayya na kungiyar G20 na shekarar 2016 a birnin Shanghai na kasar Sin. Shugaban taro na wannan karo, kuma ministan cinikayyar kasar Sin mista Gao Hucheng ya shugabanci taron, tare da yin jawabi.

A yayin jawabinsa, mista Gao ya ce, kungiyar G20 muhimmin dandalin tattaunawa ne wajen gudanar da hadin kan tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, kana tana daukar nauyi kan tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata. Jimilar cinikin waje da adadin tattalin arziki na kasashe mambobin kungiyar sun wuce kashi 80 cikin 100 da kashi 85 cikin 100 bisa na dukkan duniya, kana suna taka muhimmiyar rawa wajen inganta tattalin arzikin duniya.

Mista Gao ya kara da cewa, wannan taron ministocin cinikayya muhimmin aiki ne na shekarar Sin ta G20, yana kuma da ma'ana kwarai wajen karfafa hadin kai tsakanin kasashe mambobin kungiyar ta fuskar inganta zuba jari a fannin cinikayya.

A ganin Mista Gao, bisa yanayin tattalin arziki da ake ciki a yanzu, kungiyar G20 na juya matsayinta daga wani tsarin tinkarar kalubale zuwa wani dandalin inganta karuwar tattalin arziki. Kasashen duniya na zura ido don ganin yadda kungiyar G20 za ta iya ba da karfi wajen farfado da tattalin arzikin duniya da kuma karuwarsa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China