An gudanar da wani bangare na taron tattaunawa na shekara-shekara na Davos na kungiyar G20 a jiya Lahadi a birnin Tianjin na kasar Sin. Mai daidaita harkokin G20 na kasar Sin kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong, da mai daidaita harkokin G20 na kasar Turkiya Sinirlioglu da sauran jami'ai sun halarci taron.
Taken taron tattaunawar shi ne "sabbin matakai a wani sabon babi: fatan kasar Sin a G20". Li Baodong ya yi jawabi a gun taron cewa, Sin tana fatan za a dora muhimmanci ga kalubale da matsalolin tattalin arziki da duniya ke fuskanta, da kyautata hanyoyin samun bunkasuwa, da neman sabbin hanyoyi a wannan fanni. Kuma a kafa tsarin sarrafa hada-hadar kudi da tattalin arziki na duniya mai inganci don tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da aiwatar da ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030.
Li Baodong ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bin ka'idojin bude kofa, da fahimtar juna, da yin bayanai a bayyane karara, da sauraron ra'ayoyi daga bangarori daban daban, da yin kokari tare da bangarorin don gudanar da ayyukan share fagen taron koli na G20 da za a shirya a birnin Hangzhou na kasar Sin, da sa kaimi da samun kyakkyawan sakamako domin taron ya amfanawa duniya baki daya.
A nasa bangare, Sinirlioglu ya bayyana cewa, raguwar samun bunkasuwa da samar da kayayyaki su ne babbar matsalar tattalin arziki a duniya a halin yanzu. Shirin kyautata hanyoyin samun bunkasuwa da Sin ta gabatar shi ne hanya mai dacewa wajen warware matsalar, kana zai yi tasiri ga makomar tattalin arzikin duniya.
Hakazalika, mahalartar taron sun tattauna kan batutuwan bunkasuwar tsarin G20, da tasirin janyewar kasar Birtaniya daga EU za ta kawowa tattalin arzikin duniya da sauransu, tare da amsa tambayoyi a gun taron. (Zainab)