A yayin wani taron manema labaru da aka shirya, Mr. Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren MDD ya karanta wannan sanarwa, wadda a cikinta Mr. Ban Ki-moon ke jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da fatan wadanda suka ji raunuka za su samu sauki cikin gaggawa. Ban Ki-moon ya nanata cewa, irin wannan mataki na ta'addanci ba zai sanyaya gwiwar MDD ba, game da kara nuna goyon baya ga kokari, da kuma himmar tabbatar da zaman lafiya ta jama'ar kasar Somaliya ba.
A ranar Talata ne wani jami'in tsaron kasar Somaliya ya bayyana cewa, an kai tagwayen hare-haren ta'addanci, a wasu wurare dake dab da filin jiragen saman birnin Mogadishu, inda a kalla mutane 8 suka mutu yayin da kuma wasu da dama suka jikkata. Daga bisani kuma kungiyar Al Shabaab ta Somaliya ta ce ita ce ta kai wadannan hare-hare biyu. (Sanusi Chen)