Nkurunziza ya ce, kasarsa ta jinjinawa goyon baya da Sin ta nuna mata don warware rikicin da ya barke sakamakon babban zaben kasar, jam'iyyar FDD ta kasar Burundi tana fatan yin koyi da nasarorin da Sin ta samu wajen tafiyar da harkokin kasa, da kyautata kwarewar mulki.
A nasa bangare kuma, Duan ya ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana fatan karfafa mu'amala da jam'iyyar FDD ta Burundi, don kyautata dangantakar kasashen biyu.(Bako)