Tsagaita bude wuta a kasashen duniya mahalarta wasannin wadanda ke fama da rikice rikice wato tun daga kwanaki 7 kafin fara wasannin na Olympic zuwa kwanaki 7 bayan gama wasannin, zai taimaka wajen kara fahimtar juna da tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya.
Lykketoft, ya bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a duniya, da su amince da tsagaita bude wuta har zuwa karshen kammala wasannin na Olympic, kuma su lalibo bakin zaren warware dukkan wata takaddama cikin ruwan sanyi.
Za'a fara gudanar da wasannin Rio Olympic ne daga ranar 5 zuwa 21 ga watan Augusta, kana a gudanar da wasannin nakasassu na Olympics daga ranar 7 zuwa 18 ga watan Satumbar wannan shekara. (Ahmad Fagam)