in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNMISS ta bukaci shugabannin Sudan ta kudu su hukunta masu cin zarafin mata
2016-07-22 10:33:31 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Sudan ta kudu (UNMISS), ta bukaci shugaban kasar Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar, da su hanzarta daukar matakan ladaftar da sojojin da suka aikata laifukan yin lalata da mata a kasar.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya ce, UNMISS ta damu matuka game da samun rahotannin aikata fyade da ake zargin sojojin kasar da aikatawa kan fararen hula, har ma da yara kanana, wanda aka aikata a kusa da harabar MDD da wasu wurare da dama dake daura da babban birnin kasar Juba.

UNMISS ta rawaito cewar, an samu mutane da dama da aka ci zarafinsu, kuma an aikata wadannan mumman laifuka ne tun farkon barkewar tashin hankali na baya bayan nan a Juba a makonni biyu da suka wuce, Haq ya ce, tuni ofishin kare hakkin bil adama na MDD ya fara tattara alkaluma na wadanda matsalar ta shafa, wanda kuma laifin tamkar aikata laifukan yaki ne.

Ya kara da cewa, tawagar ta MDD na ci gaba da sintiri a yankunan domin kare fararen hula, musamman mata a birnin Juba. Har yanzu ana zaman dar dar a kasar ta Sudan ta kudu tun bayan barkewar tashin hankali na baya bayan nan a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China