Rahoton wanda hukumar gargadi game da karancin abinci wato FEW NET ta fitar, hasashen ya nuna cewar, adadin mutanen da suke fuskantar karanci abincin ya zarce kima, a kalla mutane miliyan 17 ne zasu fuskanci matsalar karancin abinci tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2017, wadanda suke matukar bukatar agajin gaggawa.
Rahoton ya ce, a karshen wannan daminar, magidanta da dama a kasashen Zimbabwe, da Malawi, da Mozambique, da Madagascar, da Lesotho, da Swaziland zasu yi matukar fuskantar karancin abinci.