in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin Najeriya sun amince da shirin tsagaita bude wuta a yakin da suke da tsagerun Niger Delta
2016-06-10 13:00:52 cri
Duk da irin hare haren da tsagerun yankin Niger Delta ke kaddamarwa kan bututan man kasar, rundunar sojin Najeriya a jiya Alhamis ta ce za ta ci gaba da tsagaita bude wuta kan tsaregun yankin Niger Delta sakamakon umarnin da gwamnatin kasar ta bayar na tsagaita bude wutar na tsawon makonni biyu.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai babban kwamandan runduna ta 82 na sojojin kasar Ibrahim Attahiru, ya fada cewar, shirin tsagaita bude wutar na mako biyu zai baiwa gwamnatin kasar damar lalubo hanyoyin warware takaddamar cikin ruwan sanyi tsakanin gwamnati da mayakan na yankin Najer Delta mai arzikin mai.

To sai dai kwamandan ya tabbatar da cewar, dakarun Najeriyar zasu komo bakin daga muddin tsagerun yankin suka ki martaba shirin tsagaita bude wutar.

Ko a ranar Laraba ma, sai da kungiyar Niger Delta Avengers ta yi ikirarin lalata wata rijiyar mai mallakar kamfanin Chevron na Amurka, dake kudancin birnin Warri duk kuwa da sanarwar dakatar da bude wutar da gwamnatin kasar ta ayyana tun da farko.

Kungiyar dai ta fada a cikin wata sanarwar cewar ba zata shiga tattaunawa da wakilan gwamantin Najeriyar ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China