Bisa sanarwar, a yayin da suke musayar wuta da 'yan kungiyar Boko Haram, sojojin Nijer sun sami taimako daga sojojin sama na hadaddiyar rundunar JTF, tare da samun babbar nasara.
A ranar 25 ga wata, gwamnatin Nijer ta tura tankuna da manyan motocin yaki sama da 10 zuwa yankin iyakar kasa tsakanin Nijer da Nijeriya domin dakile dakarun kungiyar Boko Haram, inda makasudin aikin shi ne kawar da sansanonin kungiyar dake yankin kogin Komadugu Yobe, domin kwace garin Damasak tun da wuri, garin da ake tsammanin cewa, wata muhimmiyar makarfafa ce ta kungiyar.
Bisa sanarwar da hadaddiyar rundunar JTF ta bayar, an ce, a sa'i daya sojojin Nijeriya su ma sun fara aikin yaki da kungiyar Boko Haram, domin hadin gwiwa da sojojin Nijer.(Fatima)