in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tabbatar da hari kan matatun mai a shiyyar kudancin kasar
2016-06-11 12:51:40 cri
Jiya Juma'a gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da harin da aka kaddamar kan matatun man kasar mallakar kamfanin Agip Oil a jihar Bayelsa dake kudancin kasar.

Kaddamar da hari kan bututun man ya tilasta kamfanin na Agip dakatar da aikin hako danyen mai da kamfanin ke gudanarwa wanda a kowace rana yake hako gangar danyen man fetur kimanin dubu 65.

Tunda farko kungiyar tsagerun yankin Niger Delta Avengers, sun yi ikirari cikin wata sanarwa ta shafukansu na twitter cewar sun dauki alhakin kaddamar da hare haren.

Wannan hari dai na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar na tsagaita bude wuta na tsawon makonni 2 domin tattaunawar sulhu da mayakan yankin mai arzikin mai da nufin lalubo bakin warware takaddamar cikin ruwan sanyi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China