in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsagerun NDA sun dauki alhakin lalata rijiyar man kamfanin Chevron a Najeriya
2016-06-09 12:31:21 cri
A jiya Laraba ne kungiyar tsagerun Niger Delta da ake kira Niger Delta Avengers ta bayyana cewa, mayakanta sun sake lalata wata rijitar mai mallakar kamfanin Chevron na kasar Amuirka da ke aikin hako mai a garin Warri a kudu maso gabashin kasar.

Mayakan sun lalata rijiyar man ce sa'o'i 48 bayan da gwamnatin Najeriya ta bukaci 'yan tawayen na Avengers da su tsagaita bude wuta kana su koma teburin sulhu da mahukuntan kasar.

Sai dai tun farkon kungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa,ba za ta tattaunawa da wakilan gwamnatin ba.

Har yanzu dai babu wani karin bayani daga bangaren kamfanin na Chenvron ko hukumomin kasar ta Najeriya game da harin na baya-bayan nan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China