Jami'in hukumar tsaron kasar Abayomi Olanisakin, shi ne ya tabbatar da hakan a Yenagoa, helkwatar mulkin jahar Bayelsa a loakacin da ya kai ziyarar aiki a rundunar hadin gwiwa ta sojojin kasar dake yankin Niger Delta.
Olanisakin yace, makasudun ziyarar tasa shine don cika umarnin da babban kwamandan tsaron Najeriya kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na dakile ayyukan tsagerun yankin Niger Delta.
Yace a yayin ziyarar zai binciki halin da jami'an soji a yankin suke ciki game da irin kayayyakin aiki da suke bukata domin cigaba da ayyukansu don magance barazanar dake addabar yakin mai arzikin mai. (Ahmad)