Mai magana da yawun rundunar sojin kasar kanal Sani Usman, shi ne ya tabbatar hakan a wata sanarwa ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, sanarwa ta ce wadanda aka ceto sun hada da mata da kananan yara, kuma tuni jami'an sojin suka kwashe su zuwa barikokin sojin domin ci gaba da tantance su da ba su kulawa.
Usman ya kara da cewa, rundunar sojin ta hallaka mayakan 'yan ta da kayar baya 2, amma soji uku da fararen hula 13 ne suka samu raunuka a lokacin musayar wuta a kusa da garin Gwoza.
Kawo yanzu, rundunar sojin ta yi nasarar lalata mafakar mayakan na Boko Harama masu yawa a yankuna da dama, kuma an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan an kashe mayakan 'yan ta'addan a ci gaba da simamen da dakarun Najeriyar ke yi a shiyyar arewa maso gabashin kasar. (Ahmad Fagam)