Hukumar kamfanin man fetur ta kasar Ghana GNPC, ta raka 'yan wasan domin yin ban kwana da su, a filin saukar jiragen sama, a wani mataki na ci gaba da tallafawa, da samar da kudin gudanarwa da kamfanin ke baiwa 'yan wasan, a shirin su na wakiltar kasar wajen halartar wasannin na Olympics na wannan karo.
Kungiyar 'yan wasan kasar ta Ghana dai a wannan karo, na kunshe da 'yan wasa matasa da yawa, a cewar Francis Dodoo, shugaban kwamitin Olympics na kasar, kuma matsakaitan shekarun 'yan wasan bai wuce 22 ba, cikin su hadda 'yan wasa 16, wadanda wannan ne karon farko da suke halartar gasar. Kaza lika Ghana na fatan samun nasara a gasar, bayan kwashe shekaru 24 bata samu nasarar lashe lambar Zinari ba a gasar.(Bello Wang)