160804-yan-wasan-tseren-kasar-sin-na-shirin-kafa-tarihi-a-rio-bello.m4a
|
Kungiyar ta kasar Sin ta bawa duniya mamaki a gasar lokacin zafi ta bara, yayin da suka samu lambar karramawa ta azurfa a gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta IAAF World Championships, bayan da 'yan wasan gudun kasar su 4 sun kammala gudu na tsawon mita 400 cikin dakikoki 38.01.
A baya dai kasar Sin ba ta taba kai wa matsayin zagayen karshe na wasan tseren ba da sanda a wasannin Olympics ba, sai dai a wannan karo kungiyar kasar Sin ta kunshi wasu fitattun 'yan wasan da suka hada da Xie Zhenye, wanda ya taba lashe lambar zinariya a wasan tseren mita 200 na gasar Olympics ta matasa, da Mo Youxue, tsohon zakaran tseren mita 100, a gasar 'yan wasan kwararru ta matasa, da Zhang Peimeng, gami da Su Bingtian, dan wasan Basine na farko da ya kammala gudun mita 100 cikin dakikoki 10. (Bello Wang)