Da yake tabbatar da hakan a ranar Litinin a cibiyar kula da wasannin Olympics Claudio Lima Freire hafsan hafsoshin rundunar sojojin kasar ta Brazil, ya bayyana cewa matakin da aka dauka ya nuna cewa, za a samu 'yan sanda 13,900 da za su gudanar da aikin tsaron birnin, maimakon 10,400 da aka tanada a baya.
Jami'in ya ce wasu daga cikin 'yan sanda da aka kara sun fito ne daga bangaren sa ido na rundunar 'yan sandan kasar, hakan na nufin da ma suna aiki irin na ofis, amma a wannan karo za a tura su don su shiga titunan birnin, hakan ya nuna yadda hukumar birnin Rio take dora muhimmanci sosai ga aikin tsaro a lokacin gudanar wasannin na Olympics. (Bello Wang)