Shugaban kwamitin na Slovenia Bogdan Gabrovec, ya ce matakin na IOC ya dace da manufar inganta harkokin wasanni, duk da cewa akwai matsala game da karbe aikin hukumomin kasa da kasa na sanya ido kan yanayin 'yan wasa, wanda hakan batu ne mai jan hankali..
Kaza lika Mr. Gabrovec ya ja hankalin sauran hukumomin wasannin motsa jiki na kasa da kasa, da su sauke nauyin dake wuyan su, na ganin daukacin 'yan wasa da basu da wani laifi ba, ko basu taba ta'ammali da kwayoyi masu sanya kuzari ba, sun samu damar shiga gasannin kasa da kasa yadda ya kamata.
Tsokacin Gabrovec dai na zuwa ne bayan da IOC ta yanke kudurin hana 'yan wasan kasar Rasha wadanda ake zargi da shan kwayoyin kara kuzari shiga gasar Olympic ta birnin Rio. Hukumar ta ce ya zama wajibi hukumomin wasannin kasashe daban daban su tantance 'yan wasan su domin kaucewa karya ka'idojin hukumar.(Saminu Alhassan)