in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattijan Najeriya ta musanta zargin tsige shugaban kasa
2016-07-26 09:19:51 cri
A jiya Litinin majalisar dattijan Najeriya ta tabbatar da cewar babu wani laifi da shugaba Muhammadu Buhari ya aikata wanda ya cancanci a tsige shi daga mukaminsa, a don haka majalisar ba ta da hujjar tsige shi.

Sanata Ali Ndume shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa babu wani laifi da shugaban ya aikata da ya dace a tsige shi.

A cewarsa, majalisar dattijai kadai ba ta da ikon tsige shugaban kasa, ya kara da cewar wadannan jita jitar kafafen yada labaru ne suka kitsa su.

Ndume ya ce batun tsige shugaban kasa lamari ne da ya shafi majalisun dokoki na kasa, amma ba iya majalisar dattijai ba.

A makonni biyun da suka gabata ne, wasu kafafen yada labarum kasar suka watsa rahotannin dake nuna cewa an yi yunkurin tsige shugaban kasar daga mukaminsa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China