in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta dauki matakan magance hauhawar farashi
2016-07-27 15:10:59 cri
Mahukunta a Najeriya sun bada sanarwar sauya fasalin tsarin kudaden kasar wato daga kashi 12 zuwa kashi 14 cikin 100, da nufin dakile matsalar hawa hawar farashin kayayyaki da kuma samun cigaban kasar.

Godwin Emefiele, shine shugaban babban bankin kasar CBN, ya bada sanarwar daukar wannan mataki da kwamitin tsara kudaden kasar ya yi ne, bayan taron kwanaki biyu da kwamitin yayi a Abuja. Ya ce, 8 daga cikin mambobin kwamitin su 12, sun halarci taron.

Gwamnan na (CBN) ya shedawa 'yan jaridu cewar, mutane 8 din da suka halarci zaman, 5 daga cikinsu sun goyi bayan sauya fasalin sha'anin kudaden kasar, yayin da 3 daga cikinsu suka lamunce a cigaba da amfani da tsohon tsari na kashi 12 cikin 100.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China