Bugu da kari, majalisar wakilan ta bukaci ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar, da ta sake gina tare da inganta katangun da suka kewaya gidajen yarin.
Bukatar da majalisar wakilan ta gabatar ya biyo bayan kudurin da dan majalisar Anayo Nnebe ya gabatar ne, kudurin da ya samu amincewar baki dayan mambobin majalisar.
Nnebe ya bayyana damuwa kan yawaitar fasa gidajen yari a wasu sassan kasar, musamman na baya-bayan da suka faru a garuruwan Koton Karfe, Eikiti da kuma gidan yarin Kuje.
Ya ce, yawaitar fasa gidaje yarin, wata babbar barazana ce ga tsaron kasa da ta jama'a, ganin yadda gidajen yarin kasar ba su da na'urorin tsaron da suka dace.
A saboda haka ya jaddada cewa, wajibi ne a kawo karshen wannan matsala.
Yanzu haka dai, majalisar ta umarci kwamitinta mai kula da harkokin cikin gida da ya binciki wannan batu kana ya gabatar mata da rahoto game da matakan da suka dace a dauka. (Ibrahim)