Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a yayin wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da aka shirya a garin Fatakwal da ke yankin kudancin kasar. Yana mai cewa, yanzu haka gwamnati ta mayar da hankalinta wajen sake ginawa da sake mayar da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da mahullansu zuwa gururuwansu.
Ministan wanda darekta a ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Willy Bassey ya wakilce shi, ya ce muhimmin abin da ke gabansu shi ne samar da zaman lafiya, ganin yadda jama'a suke komawa gidajensu, yayin da ita kuma gwamnati a nata bangaren take sake ginawa, da canza tunanin mutanen da rikicin ya shafa.
A cewar ministan, gwamnati tana kokarin hada kai da kafofin watsa labarai don tabbatar da cewa, an sanar da duniya abubuwan da ke faruwa a zahiri.
Minista Dambazau ya ce, Najeriya tana fama da kalubalen tsaro, wadanda suka hada da rikicin manoma da Fulani makiyaya, da na 'yan ta'adda, da satar mutane, da kungiyoyin asiri, da masu neman ballewa daga kasar, batutuwan da ministan ya ce suna bukatar duba na tsanaki daga bangaren kafofin watsa labarai.
Haka zalika ministan ya bayyana cewa, ma'aikatarsa ta bullo tare da aiwatar da wasu sabbin manufofi da nufin inganta ayyukan hukumomin tsaro guda biyar da ke karkashin ma'aikatar. (Ibrahim)